Labarai
Majalisar dokokin Kano ta bai wa Auwalu Ɗanbaba Naira miliyan ɗaya da rabi
Majalisar dokokin jihar Kano, ta karrama matashin nan Auwalu Salisu Ɗanbaba mai tuƙa Babur ɗin Adaidaita Sahu da ya mayar da kuɗin da ya tsinta a babur ɗinsa.
A zaman majalisar na yau Litinin ta bai wa matashin takardar shaidar karramawa tare da tsabar kuɗi Naira Miliyan Daya da dubu ɗari biyar.
Haka kuma majalisar, ta yi kira ga gwamnatin jihar Kano a kan ta ɗauki nauyin karatun matashin har zuwa ya kammala Sakandare da kuma Jami’a.
Makonni 4 da suka gabata ne ɗan majalisar mai wakiltar ƙaramar hukumar Doguwa Salisu Ibrahim Muhammad, ya gabatar da wani ƙudurin Ƙashin Kai watau Matter of Personal Explanation.
Yayin gabatar da ƙuɗurin wakilin ya buƙaci Majalisar kan ta karrama matashin.
Sai dai bayan gabatar da buƙatar ne a lokacin mambobin majalisar suka amince tare da yin alƙawarin cewa za su yi karo-karon kuɗi domin tallafa wa matashin.
Da ya ke gabatar da tsabar kuɗin ga Matashi Auwalu Salisu, shugaban majalisar Jibril Isma’il Falgore, ya ce, ƴan majalisar su 40 ne suka haɗa masa Naira dubu ashirin da biyar-biyar kuɗin ya kama Naira miliyan ɗaya sai kuma ita kanta majalisar da ta ba shi kyautar Naira dubu ɗari biyar.
A nasa ɓangaren, matashin Auwalu Salisu da aka fi sani da Ɗanbaba, ya gode wa majalisar tare da cewa za su yi amfani da kuɗin da ya samu wajen sayen gida.
You must be logged in to post a comment Login