Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Majalisar dokokin Kano ta buƙaci a gina titi a yankin Kumbotso

Published

on

Majalisar dokokin jihar Kano, ta buƙaci gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf, da ta gina titi a hanyar da ta tashi daga Bypass Kwanar Ƴan Shana zuwa garin Ƴan Shana har zuwa Ƴan Gizo da Limawa da kuma garu duk a yankin ƙaramar hukumar Kumbotso.

Majalisar ta buƙaci hakan ne a zamanta na yau Talata sakamakon ƙudurin da wakilin ƙaramar hukumar Kumbotso a zauren Mudassir Ibrahim Zawaciki ya gabatar.

Yayin gabatar da ƙuɗurin, Mudassir Ibrahim Zawaciki, ya yi ƙarin haske kan halin da al’ummar yankunan ke ciki.

Alhaji Mudassir Ibrahim, ya ce “Mazauna yankunan suna cikin mawuyacin hali sakamakon matsalar zaizayar ƙasa da kuma rashin kyawun hanyar shiga waɗannan yankuna”.

“Don haka ina roƙon ƴan uwana ƴan majalisa da ku taimaka ta hanyar mara wa wananna ƙuduri baya” Inji ɗan majalisar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!