Labarai
Majalisar dokokin Kano ta buƙaci gwamnati ta ɗaga darajar wasu asibitoci 4 Kumbotso

Majalisar dokokin jihar Kano ta buƙaci gwamnatin jihar da ta ɗaga darajar wasu asibitoci guda hudu zuwa manyan Asibiti a Ƙaramar hukumar Kumbotso domin sauƙaƙawa al’ummar yankin.
Dan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Kumbotso Mudassir Ibrahim Zawachiki ne ya gabatar da ƙudirin gaggawa gaban majalisar a yau, cikin Asibitocin da ya buƙaci a ɗaga darajar ta su sun haɗar da na Unguwar Sheka, Na’ibawa Chiranchi sai Mariri.
A dai zaman majalisar na yau Ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Danbatta Murtala Musa Kore, ya gabatar da ƙudirin gaggawa kan a samarwa da al’ummar yankin Gawon bature, Dan maɗaki, Telafiya, Tukurau, Gwanda wacce zata haɗe da garin Ɓabura hanya musamman a wannan lokaci na damuna ta yadda basa iya fitowa da anfanin gona.
Majalisar ta tabbatar da cewa za a miƙa ƙudirin gaba domin tabbatar da an samar wa da al’ummar yankunan sauki.
You must be logged in to post a comment Login