Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Za’a bincike kamfanin Shinkafa a Kano – Majalisa

Published

on

Majalisar dokoki ta jihar Kano ta buƙaci gwamnatin jihar da ta samar da wutar lantarki a garin Ɗan-amale zuwa Garun madad ta haɗe da garin ‘yan Guruza dukkan su a mazaɓar Madidi a ƙaramar hukumar Gwarzo.

Hakan ya biyo bayan ƙudurin da Ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Gwarzo Alhaji Yunusa Haruna Ƙayyu ya gabatar a zaman majalisar na yau Talata.

Da yake gabatar da ƙudurin Ɗan majalisr ya ce, samar da wutar a yankin abu ne mai matuƙar muhimmanci kuma zai taimaka wa mazauna yankin matuka kuma tun a baya majalisa ta 6 ta miƙa buƙatar a fara aikin amma sai sai Ɗan kwangilar ya dakatar da aikin bayan aikin ya yi nisa.

Haka dai majalisar ta buƙaci gwamnatin da ta yi amfani da wani ɓangare na kamfanin samar da taki na jihar Kano KASCO wajen ƙara gine-gine a kwalejin Fasaha dake garin Kachaco.

Majalisar ta buƙaci hakan ne bisa ƙudurin da mamba mai wakiltar ƙaramar hukumar Takai Alhaji Musa Ali Kachaco ya gabatar.

Ɗan majalisr na Takai, ya ce, samar da ƙarin gine-ginen zai taimaka wajen ƙara bunƙasa harkokin ilimi da rage zaman banza a jihar Kano.

Haka Kuma yayin zaman majalisar, Ɗan majalisa mai wakiltar Ƙaraye Alhaji Nassiru Abdullahi Dutsen Amare ya gabatar da ƙudurin neman gwamnatin jihar Kano da ta gina Titin da ya tashi daga Kwanar Kafi zuwa Nassarawa zuwa Ƙawara da Gidan Alhaji Ɗan Ango har zuwa Salihawa duk a ƙaramar hukumar Ƙaraye.

Wakininmu na majalisar dokokin Auwal Hassan Fagge, ya ruwaito mamban ƙaramar hukumar Kumbotso a majalisar Mudassir Ibrahim Zawaciki, ya gabatar da ƙudurin gaggawa na bukatar majalisar ta kafa Kwamitin bincike kan yadda wasu daga cikin ma’aikatan nan da wani kamfanin shinkafa ya tsare su suna yi masa aiki lokacin da ake cikin dokar kulle.

Da yake gabatar da ƙudurin Alhaji Mudassir Ibrahim Zawaciki, ya ce wasu daga cikin ma’aikatan kamfanin sun miƙa masa ƙorafin cewa, kamfanin ya fara korar wasu daga cikin su daga aikin inda hakan ya saba da ma tsayar da aka cimma tun a baya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!