Labarai
Majalisar dokokin Kano ta buƙaci a ɗaga likkafar Asibitin Sakatariyar NYSC da ke Takai

Majalisar dokokin Kano ta buƙaci gwamnatin jihar da ta ɗaga likkafar Asibitin sakatariyar NYSC da ke garin Takai zuwa babban Asibiti.
Ɗan majalisar mai wakilar Takai Musa Ali Kachako, ne ya buƙaci hakan ta cikin ƙudurin da ya gabatar a zaman majalisar na yau Litinin.
Shi ma da yake gabatar da nasa ƙudirin wakilin ƙaramar hukumar Kumbotso, Muddassir Ibrahim Zawaciki, ya gabatar da nasa ne kan neman gyaran hanyar da ta tashi daga sabon titin Madobi zuwa Riga-fada ta haɗe da garin Kumbotso.
Haka kuma a dai zaman majalisar na yau, ta yi wa ƙudurin gyaran dokar kotunan Shari’ar Muslunci da na kotunan ɗaukaka ƙara na shari’ar Muslunci karatu na biyu.
You must be logged in to post a comment Login