Labarai
Majalisar Dokokin Kano ta buƙaci gwamnati ta karɓe ragamar kula da matatar ruwan Bebeji
Majalisar Dokokin Kano, ta buƙaci gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf, da ta mayar da ragamar kula da matatar ruwa ta garin Bebeji daga ƙaramar Hukumar zuwa hannun jiha tare da gyara ta domin samar da ruwa a yankin.
Majalisar ta buƙaci hakan ne a zamanta na yau Talata biyo bayan ƙudurin da wakilin ƙaramar hu ta Bebeji Ali Muhammad Tiga ya gabatar.
Yayin gabatar da ƙuɗurin, ɗan majalisar ya ce, tun a shekarar 1999 da aka gina matatar ruwan zamanin mulkin Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, sai dai ba ta samun kulawa yadda ya kamata, lamarin da ya sa fiye da shekaru goma ba ta iya samar da ruwa.
Da ya ke goyon bayan ƙudurin, ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Rano Ibrahim Muhammad, ya ce, ya kamata gwamnati ta gaggauta aiwatar da buƙatar samar da ruwa a yankin na Bebeji.
Yayin zaman na yau, shugaban kwamitin kula kuɗaɗen da gwamnati ta kashe na majalisar Tukur Muhammad mai wakiltar Fagge ya gabatar da rahotonsa kan kuɗaɗen da gwamnati ta kashe musamman na aikin gina titina masu tsawo kilo mita biyar-biyar da sauran aikace-aikacen da aka yi a shekarun 2013 da 2014.
You must be logged in to post a comment Login