Labarai
Majalisar dokokin Kano ta bukaci a gina Gadar sama a shatale-talen Wapa zuwa France road
Majalisar dokokin jihar Kano ta yi kira ga gwamnati da ta gina Gadar sama a shatale-talen Wapa zuwa Faransa Road ta dangana ga junction na Katsina Road tare da samar da titin karkashin kasa daga Wapa zuwa Kofar mazugal don rage cunkuson da ake fama da shi.
Ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Fagge, Hon. Muhammad Tukur ne ya miƙa buƙatar hakan a gaban majalisar a yau Laraba.
Muhammad Tukur ya ce la’akari da yadda manya-manyan kasuwannin Kano ke wannan waje akwai buƙatar samar da hanyoyin da za su sauƙaƙawa al’umma wajen zirga-zirga.
You must be logged in to post a comment Login