Labarai
Majalisar dokokin Kano ta bukaci gwamnati da ta kwace sinadaran hada lemuka a kasuwannin jihar
Majalisar dokokin jihar Kano ta umarci kwamitocinta uku da su gudanar da bincike tare da gabatar mata da rahoto kan wata annoba da ta yadu a nan Kano a baya-bayan nan sakamakon zargin shan wasu abubuwan haɗa lemo.
Kwamitin sun hada da na: harkokin lafiya da na harkokin Kasuwanci da kuma na muhalli.
Hakan ya biyo bayan ƙudurin gaggawa da ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Bunkure Muhammad Uba Gurjiya ya gabatar yayin zaman majalisar na yau talata.
Haka kuma mambobin majalisar sun buƙaci gwamnatin Kano da ta ɗauki nauyin mutanen da suka gamu da iftila’in kasancewar wasu daga cikinsu marasa galihu ne.
Da yake gabatar da ƙudurin, Muhammad Uba Gurjiya ya buƙaci da gwamnati ta bada umarnin kwace irin waɗannan sinadarai a duk inda suke tare da kara ƙaimi wajen gudanar da bincike kan ababen ci da sha da ake shigo da su.
You must be logged in to post a comment Login