Labarai
Majalisar dokokin Kano ta bukaci gwamnati ta gyara masallacin Juma’a na cikin Birni

Majalisar dokokin jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin Kano da ta gyara tare da sake gina masallacin Juma’a na cikin Birni, tare da gyaran hanyoyin Findi da Shangu da Kurmi a kuma Yawar a ƙaramar hukumar Rano.
Ɗan majalisar Birni Aliyu Yusuf Daneji ne ya buƙaci hakan a zaman majalisar na yau, inda ya bayyana cewa tun a baya sun miƙa kudirin ga gwamnati sai dai kawo yanzu ba a kai ga fara aikin ba.
A zaman majalisar na yau, shima ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Rano, ya yi kira ga majalisar da ta buƙaci gwamnati da ta gyara wasu daga cikin hanyoyin cikin garin Rano.
Yan majalisun biyu sun bukaci gwamnatin da ta gaggauta gyaran masallacin da kuma hanyoyin la’akari da muhimmancin su ga al’umma.
You must be logged in to post a comment Login