Labarai
Majalisar Dokokin kano ta dakatar da rushe kasuwar Rano

Majalisar dokokin jihar Kano ta bada umarnin dakatar da aikin rushe kasuwar Rano da shugaban ƙaramar hukumar yake gudanarwa a wannan lokacin, da yace zai mayar da ita ta zamani.
Wannan na zuwa ne daidai lokacin da ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar ta Rano ya gabatar da ƙudirin gaggawa gaban majalisar kan yadda ƴan kasuwar ke ko kawa kan aikin, inda majalisar ta kafa kwamitin gaggawa tare da gurfanar da shugaban ƙaramar hukumar a gaban ta da yammacin talata domin jin dalilin sa na gudanar da aikin duk da irin koke koken ƴan kasuwar.
Da yake ƙarin haske ga manema labarai jim kaɗan bayan zaman farko da kwamitin yayi a yammacin talata Ɗan majalisa mai wakiltar Rano Ibrahim Muhammad Malami Rano yace yanzu haka an dakatar da aikin rushe kasuwar har sai majalisar ta gama bincike.
Da yake nasa jawabin shugaban ƙaramar hukumar ta Rano Muhammad Naziru Ya’u ya ce ya gurfana ne a gaban kwamitin domin yi musu karin haske kan rushe kasuwar inda majalisar ta dakatar da rushewa har sai ta kammala bincike.
majalisar dokokin Kanon ta gayyaci shugabancin kasuwar domin tattauna da su kan yadda aikin rushe kasuwar na su ya gudana domin samar da dai-dai to tsakani.
You must be logged in to post a comment Login