Labarai
Majalisar Dokokin Kano ta karɓi rahoton kwamitin haɗin gwiwa na kasafin kuɗi

Majalisar Dokokin jihar Kano, ta karɓi rahoton kwamitin haɗin gwiwa na kasafin kuɗi da na kananan hukumomi tare da harkokin masarautu, wanda ya shafi gyaran kasafin kuɗin shekarar 2025 na kananan hukumomi arba’in da huɗu na jihar.
Rahoton, wanda ƴan majalisa Aminu Sa’adu Ungogo Aliyu Muhammad daga Bebeji suka gabatar, ya ƙunshi shawarwari kan yadda za a inganta rabon kuɗaɗe da aiwatar da muhimman ayyuka a matakin kananan hukumomi domin tabbatar da ci gaban al’umma.
Gyaran kasafin zai bai wa gwamnati damar daidaita bukatun kowane yanki bisa ga fifikonsu, tare da tabbatar da gaskiya da adalci wajen amfani da kuɗaɗen jama’a.
You must be logged in to post a comment Login