Labaran Kano
Majalisar dokokin Kano ta katse hutun da take yi , zata dawo aiki gobe
Majalisar dokokin jihar Kano ta katse hutun da saba yi a yanzu, inda za ta dawo gobe Laraba ashirin da bakwai ga watan Nuwamba domin ci gaba da zama kamar yadda ta sabayi.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da akawun majalisar dokokin ta Kano Abdullahi Alfa ya fitar mai dauke da sa hannun daraktan yada labarai na majalisar Ali Bala Kofar Kudu.
Sanarwar ta ce majalisar ta katse hutun da ta ke yi ne wanda a baya aka tsara cewar za ta dawo domin ci gaba da zama a ranar goma sha shida ga watan gobe na Disamba domin kammala ayyukan da ke gabanta.
Sai dai sanarwar ba ta yi karin haske kan dalilai da Kuma ayyukan da suka sa majalisar ta katse hutun da ta ke yi ba domin fara zama a gobe Laraba.