Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Dalilan da suka sanya majalisa ta Kano ta dage komawa zaman majalisar

Published

on

Majalisar dokoki ta jihar Kano ta dage komawa zaman majalisar daga litinin din makon gobe har zuwa wani lokaci a nan gaba.

Hakan na cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran majalisar Malam Uba Abdullahi ya fitar a jiya Juma’a.

Sanarwar ta ce an dauki matakin ne a wani bangare na mara wa gwamnatin jihar Kano baya a kokarinta na dakile yaduwar cutar Corona.

Da yake karin haske dangane da batun dage komawa zaman, shugaban majalisar Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari, ya bukaci al’ummar jihar Kano da su rinka yin biyayya ga matakan kariya daga annobar COVID -19.

Wakilinmu na majalisar dokokin Kano Auwal Hassan Fagge, ya rawaito cewa tun a karshen watan Disamban bara ne majalisar ta tafi hutun karshen shekara, inda ta sanya ranar litinin 25 ga wannan wata na Janairu, a matsayin ranar komawa domin ci gaba da zama.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!