Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Majalisar dokokin kano tayi Alla wadai da kalaman shugaban jami’ar Bayero

Published

on

Majalisar dokokin Kano tayi All.. wadai da kalaman shugaban jami’ar Bayero Farfesa Sagir Adamu Abbas, wanda yace jami’ar ba zata saurara ba wajen daukar matakan rushe gine-ginen dake garin Rimin Zakara.

Hakan ya biyo bayan kudurin da dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Ungogo a zauren, Aminu Sa’adu Ungogo ya gabatar, na neman majalisar ta takawa jami’ar ta Bayero da wasu jami’an gwamnati da suke mara mata baya birki, akan rushe garin da suka faro, lamarin da har ya kai ga rasa rayukan mutane 4 da jikkata wasu da dama.
Dan majalisar yace yace matakin da jami’ar ta Bayero da masu mara mata baya suka dauka ya sabawa kowace irin tanadin doka a duniya.

Ungogo ya kuma kalubalanci kalaman da Shugaban jami’ar ta Bayero Farfesa Sagir Adamu Abbas yayi akan lamarin, wanda yace kalaman nasa suna nuna tsantsar rashin tausayi da daraja dan adam.

majalisar ta bukaci kwamitin ta na ƙasa daya hada hannu da kwamitin da gwamnatin Kano ta samar domin bincikar gaskiyar lamarin, tare da bukatar gwamnatin Kano ta tsananta bincike akan jami’an hukumar da suka taimakawa jami’ar ta Bayero wajen gudanar da rushe-rushen.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!