Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

An bude sabon ginin majalisar dattijai ta jami’ar Bayero

Published

on

Shugaban jami’ar Bayero mai barin gado, Faresa Muhammad Yauza Bello, ya jinjinawa kamfanin gine-gine na Usman Yahya Kansila wato UYK bisa kammala ginin sabuwar majalisar dattijai a jami’ar ta Bayero.

Muhammad Yahuza Bello ya bayyana hakan ne a yau, lokacin da ministan Ilimi Malam Adamu Adamu ke bude sabon ginin wanda shugaban hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantun kasar nan JAMB Farfesa Is-hak Oleyede ya wakilta.

Farfesa Muhammad Yahuza Bello, wanda wa’adin jagorancin shekaru biyar da ya yi a jami’ar ta Bayero zai zo karshe a ranar litinin sha bakwai ga wannan wata, ya yi fatan gwamnatoci da manyan makarantu a kasar nan su rika amfani da kamfanin gine-gine na gida mai makon amfani da kamfanonin kasashen waje.

Ya kara da cewa, la’akari da kokarin da kamfanin na UYK ya nuna wajen kammala aikin majalisar dattawan Jami’ar ta bayero cikin kankanin lokaci, kasancewar kamfanin dake ketare ne ya fara kuma ya gaza kammalashi.

A nasa jawabin shugaban kamfanin na UYK Alhaji Usman Yahaya Kansila, y ace, tun da suka fara aikin ginin na majalisar a jami’ar ta Bayero basu yi amfani da kayan kasashen waje ba, inda suka mayar da hankali wajen amfani da kayan aikin na gida, har ma da ma’aikatan dake nan Najeriya har zuwa lokacin da aka kammala aikin.

Rubutu masu alaka : 

Hotunan bikin bude ofishin majalisar dattijai a BUK

BUK zata fara gwajin masu dauke da cutar Corona

Ya kuma ce sunyi amfani da daliban da suka kammala jami’ar ta Bayero wajen gudanar da aikin ginin.

Da yake jawabin, shugaban hukumar JAMB, Farfesa Is-hak Oleyede, jinjinawa jami’ar ta Bayero ya yi, bisa yadda suke jajircewa wajen samar da ilimin da ya kamata a Najeriya, inda ya ja hankalin sabon shugaban jami’ar mai shirin kama aiki Farfesa Sagir Abbas da ya jajirce wajen rike martabar jami’ar.

Sabon ginin na majalisar dattawan a jam’ar ta Bayero an saka masa sunan tsohon shugaban jami’ar Farfesa Abubakar Adamu Rasheed, inda tsofaffin shugabannin jami’ar suka halarci taron, da suka hadar da Babban limamin Kano Farfesa Sani Zaharaddin da Farfesa Hafiz Abubakar da manyan malamai na jami’ra dana wajen ta.

Haka zalika jami’ar ta Bayero ta karrama dan jamalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Fagge, kuma shugaban kwamatin ilimi na majalisar, Honorable Sulaiman Goro, bisa irin kokari da ci gaban da yake kawowa jami’ar musamman na samar mata da gine-ginen zamani.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!