Labarai
Majalisar dokokin Kano za ta yiwa wasu dokokin jihar Kwaskwarima
Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da yi wa wasu dokoki kiranye domin yi musu kwaskwarima.
Shugaban na majalisar Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari ne ya bayyana hakan yayin zaman da majalisar ta gudanar a ranar litinin din.
Amincewar dai ta biyo bayan gabatar da kudurin gaggawa kan kirawo dokokin wanda shugaban masu rinjaye na majalisar Alhaji Labaran Abdul Madari ya gabatar yayin zaman majalisar.
Dokokin dai sun hada da dokar biyan kudaden Fansho da Garatuti da dokar ‘yancin gashin kai ga majalisar dokokin ta jihar Kano da kuma dokar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta shekarar 1962.
A wani labarin kuma, majalisar ta karbi wasika daga ofishin gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje da ya bukaci a yi gyara ga dokar tattara harajin jiha da kananan hukumomi, da kuma wasikar neman sahalewar majalisar domin yin gyara ga dokar majalisar sarakuna ta shekarar 2019 domin rage adadin mambobin majalisar sarakunan.
Shugaban na majalisar Ingr Hamisu Ibrahim Chidari ne ya shaida hakan lokacin da yake karanta wasikar a zauren majalisar a dai zaman na yau.
You must be logged in to post a comment Login