Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a majalisar dokokin Kano a 2022

Published

on

  • A shekarar ne mambobin majalisar 9 na jam’iyyun APC da PDP suka sauya sheka zuwa jam’iyyar NNPP.
  • A ranar 12 ga Oktoban shekarar ne majalisar ta amince da sauya sunan jami’ar kimiyya da fasaha ta KUST Wudil zuwa jami’ar Aliko Dangote.
  • A ranakun 22 da 23 ga Agusta majalisar ta tantance tare da tabbatar da sabbin kwamushinoni 9
  • ranar 4 ga Nuwamba gwamna Ganduje ya gabatar da kasafin 2023

A ranar 31 ga watan Janairun shekarar 2022 ne majalisar dokokin jihar Kano ta sahale wa gwamnagandujae damar gina gidaje guda 5,000 ga malamai tare da sauran kananan ma’aikata.

Haka kuma a ranar 21 ga faburairun shekarar ne majalisar ta bukaci gwamnatin Kano da ta samar da kwalejin nazarin aikin noma a garin Ghari da ke karamar hukumar Kunchi.

A ranar 28 ga watan na Faburairu kuwa, majalisar ta ki amincewa da wasikar da ofishin babban mai binciken kudi na jiha ya aike mata da ke bukatar nada Alhaji Isma’il Musa a matsayin babban mai binciken kudi.

Ha kuma a ranar 15 ga watan Yunin shekarar da muka yi bankwana da ita ne majalisar ta sahale wa gwamnatin Gamduje damar ciyo bashin Naira biliyan 10 domin saye tare da kakkafa na’urorin CCTV domin inganta tsaro.

Haka dai a ranar 20 ga watan nan Yuni ne mambobin majalisar su 28 suka zabi wakilin karamar hukumar Ƙiru Alhaji Kabiru Hassan Dashi, a matsayin sabon mataimakin shugaban majalisar.

Jim kadan bayan zabar ta sa, Kabiru Hassan Dashi ya sha rantsrwar kama aiki daga daraktan harkokin shari’a na majalisar Barrister Nasidi Aliyu, tare da gode wa Allah bisa samun damar.

A dai ranar 12 ga Oktoban shekarar ta bara ne, majalisar dokokin ta Kano ta amince da sauya sunan jami’ar kimiyya da fasaha ta garin Wudil zuwa jami’ar Aliko Dangote.

A ranar 8 ga Agusta kuwa, maajalisar ta umarmarci kwamitinta na harkokin wasanni da ya gudanar da bincike kan matsalolin da suka janyo wa Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ficewa daga gasar Firimiya ta kasa.

A ranar 11 ga watan na Agusta kuwa, majalisar dokokin ta sahale kudurin kotunan sulhu ta shekarar 2021 zuwa doka.

A dai shekarar da muka yi bankwana da ita ne a ranakun 22 da kuma 23 ga Agusta, majalisar ta tantance tare da tabbatar da sabbin kwamushinoni 9 da gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya tura wa majalisar ta cikin wasikun da ya aike wa majalisar.

Sababbin kwamishinonin sun hada da: Ibrahim Dan’azumi, Abdulhalim Abdullahi, Lamin Sani-Zawiyya,Ya’u Abdullahi-Yan’shana, Garba Yusuf Abubakar, Dr Yusuf Jibirin, Adamu Fanda, Saleh Kausani, Dr Ali Burum Burum da kuma Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa.

Bugu da kari, a dai ranar 29 ga watan Agusta, majalisar ta sahale kudurin kayyade adadin kayan da manyan motoci za su dauka ta bara zuwa doka, kana a dai ranar ta kuma kafa kwamitin wucin gadi da zai gudanar da bincike domin lalubo hanyoyin magance matsalolin ambaliyar ruwa a kasuwar Kantin Kwari da sauran sassan jiha.

A ranar 20 ga watan Oktoban bara kuwa, majalisar dokokin jihar Kano ta sahale kudurin dokar kare gurbatar muhalli ta shekarar 2022, tare da tabbatar da sake nada Alhaji Dahiru Abbas Kachako

da Abdallah Abbas amatsayin kwamishinoni a hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano KANSIEC.

A ranar 4 ga watan Nuwamba ne gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya gabatar wa majalisar kasafin bana.

Rubutu mai alaka: https://freedomradionig.com/yanzu-yanzu-ganduje-zai-gabatar-da-kasafin-ku%c9%97in-2022/

Haka kuma a ranar 15 ga Nuwamban bara ne majalisar ta sahale dokar samar da asibitin koyarwa na Muhammad Abdullahi Wase ta shekarar 2022, tare da amincewa da rahoton kwamitinta na iliimi, kan samar da dokar jami’ar ilimi ta Sa’adatu Rimi ta shekarar 2022.

Haka dai a ranar 16 ga watan Nuwamba ne majaliisar ta sahale gyran dokar mutane masu bukata ta musamman karo na biyu ta shekarar 2022.

A dai ranar ne majalisr ta amince da raoton kwamitinta na kasafin kudi kan kwarya-kwaryan kasafin kudi na shekarar ta 2022.

A ranar 1 ga watan Disamban 2022 ne majalisar dokokin jihar Kano, ta gudanar da taron jin ra’ayin jama’a a kan dokar kare hakkin kananan yara.

Haka kuma, a ranar 15 Disamban 2022 majalisar ta gudanar da taron sauraron ra’ayin jama’a a kan kasafin bana.

A dai watan na disamban bara, a zaman majalisar na 19 ga wata, ta amince da yin kiranye ga dokar Fansho da Garatuti da dokar hukumar lura da ayyuan majalisar da kuma dokar zirga-zirgar ababen hawa domin yi musu kwaskwarima.

Haka kuma a dai ranar ce majalisar ta karbi wasiku biyu daga gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje, da yake bukatar majalisar ta yi gyara ga dokar karbar kudaden harajin jiha da Kananan hukumomi da kuma dokar masarautar Kano ta shekarar 2019 kamar yadda shugaban majalisar Engr. Hamisu Ibrahim Chidari ya sanar yayin zaman.

Haka dai, a ranar 29 ga Disamba, majalisar dokokin jihar Kano, ta sahale kasaafin bana da ya haura naira Miliyan 268 da Miliyan 197 da dubu 731 zuwa doka.

A dai shekarar da muka yi bankwana da ita ne mambobin majalisar su 9 na jam’iyyar APC da na PDP suka sauya sheka zuwa jam’iyyar NNPP.

wadanda suka sauya shekar sun hada da: mataimakin shugaban majalisar na lokacin Alhaji Zubairu Hamza Massu mai wakiltar Sumaila da shugaban marasa rinjaye na lokacin Isiyaku Ali Danja, da mataimakin shugaban masu rinjaye na lokacin Abdullahi Iliyasu Yaryasa, da Muhammad Bello Butu-butu wakilin R/Gado da Tofa da wakilin Kumbotso a zauren Mudassir Ibrahim, da Tukur Muhammad na Fagge da wakilin karamar hukumar Nasarawa Umar Musa Gama, sai Aminu Sa’adu mai wakiltar Ungogo da kuma Alhaji Garba Shehu Fammar mai wakiltar karamar hukumar Kibiya.

Sai dai an samu wasu mambobin majalisar 3 da suka sauya sheka a bana daga jam’iyyar NNPP zuwa APC, mambobin sun hada da walilin laramar hukumar Dawakin Kudu Mu’azzam Elyakub da Abubakar Uba Galadima wakilin Bebeji da kuma wakilin karamar hukumar Birni Salisu Maje Ahmad Gwangwazo.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!