Labarai
Majalisar dokokin ta bukaci gwamntin jida da ta kawo wa al’ummar Alajawa a Shanono dauki
Majalisar dokokin jihar Kano ta bukaci gwamnatin jiha da ta kai daukin gaggawa ga al’ummomin da ke mazabar Alajawa a yankin karamar hukumar Shanono sakamakon barnar da ruwan sama kamar da bakin kwarya ta yi musu.
Hakan ya biyo bayan kudirin gaggawa da dan majalisa mai wakiltar mazabar Bagwai da Shanono Ali Ibrahim Isah Shanono ya gabatar yayin zaman majalisar na jiya.
Da ya ke zantawa da manema labarai bayan zaman majalisar Ali Ibrahim Shanono wanda shine shugaban kwamitin kula da ilimi mai zurfi na majalisar, ya ce; ruwan da aka yi a makon jiya yayi matukar barna ga jama’ar yankin.
A wani labarin kuma kungiyar Kanawa educational foundation for disable ta yi kira ga gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da ya gaggauta sanya hannu kan dokar masu bukata ta musamman da majalisar dokokin jihar Kano ta sahalewa a jiya.
Shugaban kungiyar Abba Sarki Sharada ne ya bayyana haka ga manema labarai a farfajiyar majalisar dokokin jihar Kano a jiya.
Wakilin mu Abdullahi Isah ya ruwaito shugaban majalisar dokokin na Kano Yusuf Abdullahi Ata na cewa, da zaran dokar ta fara aiki za ta taimaka gaya wajen kyautata rayuwar mutane masu bukata ta musamman