Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Dr Ibrahim Musa:Cutar rashin tsayawa jini na iya kisa farat daya

Published

on

Wani kwararren likita anan Kano Dr. Ibrahim Musa, ya ce; cutar rashin tsayawar jini tana iya kisa farat daya, sakamakon hatsarin da cutar ke dauke da ita.

Dr. Ibrahim Musa wanda likita ne a sasahen kula da jini a Asibitin koyarwa na Aminu Kano, ya bayyana hakan ne yayin zantawarsa da wakiliyar Freedom Radiyo Aisha Muhammed Yelleman a wani bangare na bikin ranar cutar rashin tsayawar  jini ta duniya.

Ya ce, taimakon farko da ake yiwa masu dauke da wannan cuta shine yin allura da ke daskarar da jini bayan an samu rauni, sai dai a cewar sa ba kowa ne ke iya sayaba sakamakon tsadar sa.

Hukumar lafiya ta duniya WHO ce dai ta ware ranaR 17 ga watan Afrilun kowacce shekara a matsayin ranar rashin tsayawar jini ta duniya.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!