Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Majalisar Kansiloli: Ta dakatar da shugaban karamar hukumar Kumbotso

Published

on

Majalisar kansiloli ta karamar hukumar Kumbotso da ke nan Kano, ta dakatar da shugaban karamar hukumar Alhaji Kabiru Ado Panshekara bisa zarginsa da karkatar da wasu kudade.

A baya-bayan nan ne dai hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, ta tsare shugaban karamar hukumar ta Kumbotson, bisa tuhumar sa da amfani da karfin kujerarsa wajen karkatar da tallafin kayan masarufin gwamnati na ragewa jama’a radadin dokar hana su fita saboda annobar coronavirus.

Yanzu haka dai bayan dakatar da Alhaji Kabirun da majalisar Kansilolin ta yi, haka zalika ta kuma bukaci majalisar dokokin jihar Kano da ta yi bincike kan dakataccen shugaban karamar Hukumar da take zargin ya yi babakere kan kudaden.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!