Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Zamba Cikin Aminci: Shugaban KAROTA zai gurfana a gaban kotu

Published

on

A yau ne ake sa ran shugaban Hukumar KAROTA Baffa Babba Dan-Agundi zai gurfana gaban kotun majistiri da ke nan Kano, sakamakon zargin sa da aikata zamba cikin aminci da kuma yaudara.

Kuma kamar yadda kotun ta bayar da umarni, shugaban na KAROTA da kan sa take son gani a gabanta ba wani wakilinsa ba, sakamakon girman laifin da ake zarginsa da aikatawa.

Kotun karkashin mai shari’a Muhammad Jibril ta gayyaci Baffa Babban ne biyo bayan karar da wasu direbobin baburan adaidata sahu su ka shigar a gaban ta, bayan da suke zargi an yaudare su kan wata na’ura da aka karbe musu kudade da sunan za a basu.

Barister Abba Hikima, kwararren lauya anan Kano, wanda kuma ke wakiltar masu gabatar da karar shugaban Hukumar KAROTA Baffa Babba Dan-Agundi bisa zargin aikata zamba cikin aminci da kuma yaudara.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!