Kaduna
Majalisar kolin shari’a ta kasa reshen jihar Kaduna ta yi Allah-wadai da kalaman Rabaran Matthew Hassan Kukah

Majalisar kolin shari’a ta kasa reshen jihar Kaduna ta yi Allah-wadai da kalaman Rabaran Matthew Hassan Kukah, wanda yace aiwatar da dokar Shari’ar Musulunci a arewacin kasar nan shi ne ya haifar da tashe-tashen hankula a yankin. Majalisar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da sakataren ta Engr. AbdurRahman Hassan ya fitar.
A cikin takardar sanarwar ya bayyana kalaman Matthew Hassan a matsayin rashin adalci, inda yace ya manta da tarihi da kuma manufar shari’ar Musulunci a yankin.
Majalisar ta kara da cewa kalaman Hassan Kukah sun nuna gazawarsa a kan fahimtar mahimmancin shari’ar Musulunci a arewacin kasar nan.
You must be logged in to post a comment Login