Labarai
Majalisar ta umarci Rundunar Soji ta aika karin jami’ai Maiduguri da Yobe

Majalisar Dattawan Najeriya, ta bukaci rundunar soji da ta gaggauta aika karin dakaru zuwa jihohin Borno da Yobe, bayan sake bullar hare-haren Boko Haram a yankunan.
Daukar wannan mataki na zuwa ne bayan sake bullar sabbin hare-haren kungiyar a yankunan Arewa maso gabashin kasar.
Majalisar ta dauki matakin ne bayan gabatar da wani kudiri da babban mai tsawatarwa na majalisar, Sanata Tahir Munguno ya gabatar.
Haka kuma, Majalisar ta amince da hadin kai tsakanin jamai’an tsaro da masu sa kai don kawar da ayyukan kungiyar.
Ko a ranar Litinin din makon nan wani hari da kungiyar Boko Haram ta kai wani sansanin Sojoji da ke garin Marte a karamar hukumar Munguno ya yi sanadiyyar kashe sojoji da dama.
You must be logged in to post a comment Login