Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Majalisar wakilai ta amince Buhari ya ayyana ƴan bindiga a matsayin ƴan ta’adda

Published

on

Majalisar wakilai ta buƙaci shugaban ƙasa Muhammdu Bahari ya ayyana ƴan bindigar da suka addabi ƙasar nan da ma waɗanda suke ɗaukar nauyin su a matsayin ƴan ta’adda.

Bukatar majalisar wakilan ta yi daidai da ta majalisar dattijai da ta gabatar a ranar Laraba.

Shugaban kwamitin harkokin tsaro na majalisar Babajimi Benson ne ya buƙaci hakan a zaman ta na ranar Alhamis.

Shugaban majalisar Femi Gbajabiamila ya tambayi ƴan majalisar ko da mai ƙalubalantar ƙudurin? Sai dai dukkanin su sun amince da buƙatar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!