ilimi
Majalisar Wakilai ta gargadi hukumar WAEC

Majalisar Wakilan Najeriya, ta gargadi Hukumar Shirya Jarrabawa ta WAEC kan shirin da ta ke yi na fara yin amfani da kwamfuta daga shekara da ke tafe ta 2026, tana mai cewa hakan na iya janyo yawan faduwar dalibai idan ba a shirya tsaf ba kafin aiwatar da sabon shirin.
Ɗaya daga cikin mambobin majalisar ya bayyana cewa, yawancin makarantu a sassan ƙasar nan basu da kayan aiki da kuma horo da zai bai wa ɗalibai damar yin irin wannan jarrabawa ta kwamfuta cikin sauƙi.
Majalisar ta bukaci WAEC da ma’aikatar ilimi ta ƙasa da su tsara hanyoyin horar da malamai da ɗalibai tun daga yanzu, domin kaucewa matsaloli.
You must be logged in to post a comment Login