Labarai
Majalisar wakilai ta sha alwashin kawo karshen masu safarar miyagun kwayoyi

Kwamitin wucin gadi na majalisar wakilai da ke bincike kan karuwar safarar miyagun kwayoyi da shaye-shaye ya sha alwashin zakulo wadanda suke aikata laifin domin gurfanar da su a gaban kotu domin tabbatar da tsaro da kare lafiyar mutanen Najeriya.
A wata sanarwa da ya fitar, shugaban kwamitin Timeyin Adelegbe, ya ce, ba za su bari Najeriya ta zama wani babbban sansanın sayar da kayan maye da haramtattun kwayoyi, da cin zarafi, da sauran miyagun laifuka ba.
Dan majalisar ya kuma sanar da cewa, kwamitin na ci gaba da shirya wani taron masu ruwa da tsaki a Abuja da Lagos domin tattaunawa da tattara bayanai daga ‘yan Najeriya kan yadda za a kawo karshen wannan barazana.
You must be logged in to post a comment Login