Kasuwanci
Majalisar Wakilai za ta shiga tsakani a rikicin PENGASSAN da Dangote

Majalisar Wakilai, ta kuduri aniyar shiga tsakani a rikicin da ya barke tsakanin kungiyar manyan ma’aikatan man fetur da iskar gas PENGASSAN da Kamfanin mai na Dangote, wanda ya haifar da tsaikon rarraba mai a fadin Najeriya.
Ɗaukar wannan mataki ya biyo bayan kudirin gaggawa da ‘yan majalisar Alhassan Ado Doguwa daga Kano da Abdussamad Dasuki daga Sakkwato suka gabatar.
Majalisar ta jaddada muhimmancin masana’antar Dangote ga ci gaban tattalin arzikin Najeriya, inda ta bukaci da a kare masu zuba hannun jari daga rikicin ƙungiyoyin ma’aikata.
You must be logged in to post a comment Login