Labarai
Majalisar wakilai zata binciki manyan ayyukan gwamnatin tarayya tun daga 1999
Majalisar wakilan kasar nan ta yanke shawarar bincikar manyan ayyukan raya kasa na gwamnatin tarayya da aka watsar tun daga shekarar 1999 zuwa yanzu.
Ayyukan wadanda majalisar ta kiyasta cewa sun kai kimanin 20,000, kuma kudinsu sun haura biliyoyin nairori, da yawa daga cikin ‘yan kwangilar sun watsar da ayyukan ne duk kuwa da cewa an biyasu akalla sama da kashi 50 na kudin aikin.
Matakin majalisar ya zo ne bayan da a jiya laraba dan majalisa Francis Uduyok ya gabatar da kudurin bukatar yin hakan, inda ya samu goyon bayan ‘ya’yan majalisar baki-daya.
Francis Uduyok ya bayyana cewa ayyukan da aka watsar sun zama wata hanyar zirarewar kudin gwamnati sakamakon yadda ake ninka farashin aikin da zarar gwamnatin ta yi kudurin sake farafado da su.
A gefe guda kuma majalisar ta bukaci gwamnatin tarayya da ta aiwatar da gyara tare da samar da kayayyakin aiki a asibitin kashi na Igbobi da ke Jihar Lagos da kuma irinsa da ke garin Daura a Jihar Katsina.
Matakin ya biyo bayan kudurin da dan majalisa Ademorin Kuye ya gabatar, wanda ya samu goyon bayan majalisar