Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Majalisar zartarwa ta Kano ta shiga taron gaggawa

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce a yanzu haka ta kammala shirye shiyen ta na almajiran da zaa sanya a makarantun tsangaya da ke mazabun majalisar dattawa uku an an Kano.

Gwamnan Ganduje ya bayyana hakan ne gabanin fara taron majalisar zartarwa a yau wanda aka saba gudanawar a ranar Laraba, sai dai kwatsa ham aka kira taron a yau Litinin.

Ya kara da cewa a yanzu haka dukkan shirye-shiryen makarantun tsangayar sun kammala sai dai akwai sauran gyare-gyare da ake yi.

Wakiliyar mu ta fadar gwamnatin Kano Zahrau Nasir ta ruwaito cewa tun dai da safiya yau din ne jamian tsaro ke ta shigowa fadar gwamnatin ta Kano in da kuma Gwamnan ya ce zasu cigaba da taron majalisar zartarwar kafin daga baya a sake Kiran yan jaridun.

Kafin fara taron dai gwamnan Abdullahi Umar Ganduje ya yi wa manema labarai jawabi kan yadda zaman majalisar zai kasance.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!