Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Talakawa sun yi Al-kunuti kan yunkurin tsige Sarkin Kano

Published

on

Dandazon jama’a ne suka gudanar da sallar alkunuti da addu’o’I a harabar babban masalacin Juma’a na Kano, kan yunkurin gwamnatin Kano na tsige Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II.

Mutanen wadanda ke rike da kwalaye masu dauke da bayanan kira ga gwamnatin Kano kan ta mayar da hankali wajen yin ayyukan more rayuwa ga al’umma mai makon mayar da kai kan yunkurin tsige Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na II.

Jim kadan bayan kammala sallar ne kuma sai aka gudanar da addu’o’I na musamman don neman Allah ya kawo dai-daito kan rikicin dake tsakanin masarauta da gwamnatin jihar Kano.

Wasu daga cikin masu addu’o’in sun shaida Freedom Rediyo cewa sun fito ne a matsayin su na masu kishin jihar Kano, kuma basa jin dadin abubuwan da suke faruwa, indan hakan ya cigaba da afkuwa ba zai haifarwa da jihar Kano ‘da mai ido ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!