Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Majalisar zartaswa ta amince da baiwa shirin harkokin sufuri na jihar lagos bashin Dala miliyan 20

Published

on

Majalisar zartarwa ta kasa ta amince da baiwa shirin manufofin harkokin sufuri na jihar Lagos bashin Dala miliyan 20 wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoran ta a yayin taron mako-mako.

 

Kudin na daya daga cikin basukan da majalisar ta taba amincewa ta baiwa jihar Lagos da ya kai Dala miliyan 247.

 

Ministan kudi Hajiya Zainab Ahmed ta sanar da hakan jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwar wanda aka yi a fadar shugaban kasa a jiya Laraba.

 

Hajiya Zainab Shamsuna Ahmed ta ce majalisar ta amince da baiwa jihar Lagos bashin ne ganin shirin zai samarwa mazauna jihar aikin yi fiye da miliyan daya da dubu dari 800,kuma gwamnatin tarrayya na da karfin gwiwar jihar na da karfin gwiwar biyan kudin cikin lokaci.

 

Daga cikin ministocin da suka yi wa ‘yan jaridu masu aiko da rahotanni daga fadar gwamnati akwai minsitan sufuri Rotimi Amaechi da ministan babban birnin tarayya Abuja Bello Mohammed da mai taimakawa shugaban kasa kan kafafan yada labarai Garba Shehu.

 

Ministan kudin ta yi bayanin cewar,bashin da ake bin Najeriya bai wuce kima ba, yana nan kadaran-kadahan., kuma sauran bashin dala miliyan 20 na 3 da za’a baiwa jihar Lagos an same shi ne daga hukumar raya kasashe ta kasar Faransa, an nemo shi ne don inganta rayuwar ‘yan jihar Lagos dake rayuwa a birnin na Lagos wanda akasarin sun na zaman kashe wando.

Yayin da ak son ganin an bunkasa harkokin sufuri a jihar ta Lagos da ma kasa baki daya.

 

 

 

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!