Labarai
Majalisar zartaswa ta amince da fitar da biliyan 192 da miliyan dari 900 don biyan ‘yan kwangilar da za su yi gyaran tituna
Majalisar zartaswa ta kasa ta amince da a fitar da naira biliyan dari da casa’in da biyu da miliyan dari tara domin biyan ‘yan kwangila da za su gudanar da gyaran wasu tituna da kuma gadaje a kasar nan
Karamin ministan samar da wutar lantarki ayyuka da gidaje Mustapha Baba Shehuri ne ya bayyana haka jim kadan bayan kammala taron majalisar zartaswa ta kasa wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a fadar Asorok.
A cewar ministan cikin titunan da aka ware kudaden dominsu sun hada da: titi mai nisan kilomita goma sha shida da digo bakwai da gada mai tsawon mita goma sha biyar wanda ya hada garuruwan Suleja da Chaaza da Banguru zuwa Rafin Sanyi duk a jihar Niger akan kusan naira biliyan shida.
Haka zalika majalisar zartaswar ta kuma amince da a fitar da naira biliyan dari da talatin don mai da titunan da ya hada garuruwan Jebba da Ilorin da Mokwa zuwa Bokani da ke cikin jihar Niger da Kwara mai hannu biyu.
Majalisar ta kuma ba da kwangilar aikin gadar Ibi da ke kogin River Benue wanda ya hada garuruwan da ke jihohin Taraba da Benue akan kudi naira biliyan hamsin da bakwai.
Mustapha Baba Shehuri ya kuma ce nan ba da dadewa ba gwamnati za ta fara aikin kebabbun wuraren bunkasa kasuwanci a jihohin Lagos da Katsina da Abia da Calabar da kuma Kano.