Kiwon Lafiya
Majalisar zartaswa ta amince da jinginar da rubunan abincin 20 daga cikin 33 na Najeriya
Majalisar zartarwa ta kasa ta amince ta jinginar da rubunan abincin 20 daga cikin 33 da take da su ga bangarori masu zaman kan su har ma da ‘yan kasuwa akan Naira biliyan 6 gaba ki dayan su.
Ministan gona da raya karkara Chief Audu Ogbeh ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala taron majlisar zartarwa da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a fadar gwamnati dake Abuja da aka yi a Jiya Laraba.
Chief Audu Ogbeh ya ce rubunan adana abincin dake sassan kasar nan za’a jinginar da su ne na shekaru 10, ga ‘yan kasuwa ko kuma bangarori masu zaman kansu dake son sha’awar karba, yana mai cewar ya gabatar da kudirin sa a gaban majalisar zartarwar ne don neman sahalewar shugaban kasa da ma daukacin ‘yan majalisar kasancewar hakan zai bunkasa tattalin arzikin kasar nan
Ministan gonar ya kara da cewar, rubunan adana kayayyakin da aka fi sani da Silos a turance guda 33 na da karfin tan miliyan daya da dubu dari uku da sittin kowannen sa kuma suna cikin shiyoyin kasar nan guda 6 da gwamnatin tarayya ta mallaka amma kuma an yi watsi da su.
Ya ce a shekara ta 2014 gwamnati mai ci a wancan lokacin ta yi niyyar saida su, amma kuma daga bisani ta yanke shawarar jinginar da su ga ‘yan kasaiwa don samarwa gwamnati kudaden shiga.