Kiwon Lafiya
Majalisun dokokin kasar nan ta ce rundunar yan sanda na jan kafa wajen kammala bincike
Majalisun dokokin kasar nan sun nuna rashin jin dadinsu kan yadda rundunar ‘yan-sanda ke jan kafa wajen kammala bincikenta na yadda wasu tsageru suka farwa Majalisar Dattijai da tsakar rana tare das ace sandar girma ta Majalisar.
Kwamitin hadin gwiwa na Majalisun dokokin kasar nan karkashin jagorancin Sanata Bala Ibn Na-Al..da kuma ‘yar-majlisar wakilai Betty Apiafi ne ya bayyana hakan lokacin da Kwamishinan ‘yan-sanda mai gudanar da binciken Abu Sani ya bayyana gaban kwamitin.
Abu Sani ya shaidawa kwamitin cewa har yanzu basu kammala bincikensu ba, sai dai ya bada tabbacin cewa sun nisa cikin binciken, kasancewar wadanda aka kama din sun musanta zargin da ake mu su na hannu a ciki.
Ya kuma bayyana cewa na’urar daukar hoto da kurilla wato CCTV ta zauren Majalisar ta daina aiki wato dai ba ta dauki hoton faruwar lamarin ba.
A ranar 18 ga watan Afrilun da ya gabata ne wasu tsageru 5 suka kutsa kai cikin zauren Majalisar dattijan tare da yin awon gaba da sandar girma ta majalisar.
Shi kuwa Sanata Ovie Omo-Agege bai ce komai lokacin da ya bayyana gaban kwamitin bayan da ya ce maganar ta na gaban Kotu, yayin da Sanata Ali Ndume ya musanta duk wani zargi da aka yi ma san a hannu cikin al’amarin.