Connect with us

Labarai

Majlisar Kano ta musanta zartar da dokar dandatsa

Published

on

Majalisar dokokin jihar Kano ta musanta cewa ta zartar da dokar yin dandatsa ga mutanen da aka kamasu da laifin fyade.

Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Dala Lawan Husaini Chediyar ‘Yan-Gurasa ne ya bayyana haka yayin zantawa da tashar freedom rediyo.

Ya ce, an dai gabatar da kudirin gaban majalisar a kwanakin baya, sannan sai anji ra’ayin al’umma kafin a dauki mataki kan lamarin.

Ya kuma ce, majalisar za ta tsats-tsefe kudirin sosai kafin amince da shi.

Dan Majalisar ya kara da cewa masu ruwa da tsaki da suka hada da malamai da sarakuna za su taka rawa wajen tabbatar da wannnan doka .

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,909 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!