Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Makabartar mu ta cika gwamati ta kawo mana dauki – Al’ummar Hotoro

Published

on

Jama’ar unguwar Hotoro NNPC, sun koka tare da bukatar gwamnatin jihar Kano da ta kawo musu dauki domin gyara Makarbar yankin  wacce ta cika a halin yanzu.

A cewarsu a yanzu haka ba sa da inda za su binne gawarwaki in anyi mutuwa a unguwar sakamakon cikewa da makabartar ta yi.

Shugaban kwamitin ci gaban unguwar ta Hotoro NNPC Malam Garba Hussein Isyaku ne ya yi wannan kiran yayin gangamin aikin gyara makabartar da suka gudanar da safiyar yau Asabar.

Ya ce, a baya al’ummar yankin sun yi bakin kokarin su , inda gwamnatin jiha tayi musu alkawarin basu fili, amma kawo yanzu lamarin ya ci tura.

Wasu daga cikin dattijan yankin, sun yi karin bayani dangane da yadda lamarin makabartar yake a halin yanzu, inda suka ce sun dade suna bibiyar gwamnatin don ganin ta saya musu filayen da ke makwabtaka da makabartar don a fadada ta.

Wakilinmu Aminu Halilu Tudunwada, ya ruwaito cewa al’ummar yankin , sun bukaci gwamnati da masu hannu da shuni da su shigo cikin lamarin don taimaka musu

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!