Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kungiyar lauyoyi reshen jihar Bauchi tayi barazanar kin halartar taron shekara

Published

on

Kungiyar lauyoyi ta kasa NBA reshen jihar Bauchi, ta bi sahun takwararta ta jihar Jigawa wajen barazanar kin halartar babban taron shekara-shekara da uwar kungiyar ta kasa ta shirya matukar ba a dawo da gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai cikin bakin da za su gabatar da mukala a yayin taron ba.

Haka zalika kungiyar ta NBA reshen jihar Bauchi ta bukaci uwar kungiyar ta kasa da ta bai wa mambobin kungiyar na jihohi hakuri sakamakon daukar wannan tsastsauran mataki kan gwamnan na kaduna ba tare da sahalewarsu ba.

A cikin wata sanarwar mai dauke sa hannun shugaban kungiyar reshen jihar Bauchi Abubakar Abdulhamid da sakatarensa Shamsuddin Magaji, kungiyar ta barranta kanta daga daukar waccan mataki da uwar kungiyar ta yi.

Saboda haka kungiyar ta lauyoyi reshen jihar Bauchi ta ce ko dai uwar kungiyar ta janye matakin da ta dauka akan gwamnan na Kaduna ko kuma ta kauracewa halartar taron.

Tun bayan daukar matakin dai ake ta samun sabanin ra’ayi game da tsame sunan gwamna Nasir Elrufai daga cikin wadanda za su gabatar da jawabi a wajen taron na kungiyar lauyoyi wadda uwar kungiyar ta ce ta dau matakin ne ba da wata manufa ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!