Labarai
Makon muhalli: Mun Kwashe Shara Tan 4,300 a Kwanaki 13 – Dr. Kabiru Getso
Gwamnatin jihar Kano ta ce ta kwashe shara da yawanta ya kai tan dubu 4 da ɗari 300 cikin kwanaki 13 a sassa daban daban na jihar.
Kwamishinan Muhalli Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya bayyana hakan lokacin da ya jagorancin duba yadda aikin ya kasance.
Dakta Kabiru Getso ya ce, shirin makon muhallin na wannan shekarar da aka fara a ranar 16 ga Afirilun 2022, an kwashe sama da Tifa 787 na shara, adadin da ya kawo Tan dubu 4 da ɗari 300.
Wararen da aka kwashe tarin bila kuwa sun haɗar da: Yakasai, kofar Mata Bola “masallacin idi” a Karamar hukumar da Koki da Sarari da kuma Dandago dake Karamar hukumar Gwale dukkansu a cikin kwaryar birnin Kano.
“Shi Shirin an Samar da shi ne domin kwashe dinbin sharar da tayi yawa a cikin ƙwaryar Birnin Kano biyo bayan umarnin da gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayar na a gaggauta kwashe sharar.
“Mun shirya kammala aikin ne cikin kwanaki 10, saboda mu inganta shi sai muka ƙara kwanaki a kai kasancewar bikin ƙaramar Sallah na ƙaratowa” a cewar Getso.
Kwamishinan ya buƙaci al’umma da su guji zuba shara a magudanan ruwa, tare da Tsaftace muhallan su yadda ya kamata.
You must be logged in to post a comment Login