Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Malami ya dakatar da daraktoci 12 a EFCC

Published

on

Ofishin attorney janar na kasa kuma ministan shari’a ya dakatar da wasu daraktoci guda goma sha biyu a hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC.

Rahotanni sun ce ofishin attorney janar na kasar ya turowa mai rikon mukamin shugabancin hukumar ta EFCC Muhammed Umar da wasikar dakatar da daraktocin ne a daren jiya Talata.

A cewar takardar dakatarwar hakan wani mataki ne da zai taimaka wajen gudanar da cikakken bincike kan ayyukansu a hukumar ta EFCC.

Ya zuwa yanzu dai dakataccen hukumar ta EFCC Ibrahim Magu ya shiga mako na biyu da gurfana a gaban kwamitin shugaban kasa da ke gudanar da bincike akansa game da zarginsa da laifuka da dama.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!