Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Malawi ka iya rasa buga wasan ta da Ivory Coast

Published

on

Turka turkar da ta kunno kai tsakanin Gwamnatin ƙasar Malawi da hukumar Kwallon ƙafa ta ƙasar , na ka iya shafar wasan kasar da zata fafata da kasar Ivory Coast na gasar neman tikitin shiga gasar kofin Duniya na shekarar 2022.

Hakan ya biyo Bayan da mahukuntan kwallon kasar suka bukaci gwamnati data bada kudaden da kungiyar Kwallon kafa ta kasar zasu yi shirye shiryen tunkarar wasan da zata fafata da Ivory Coast gida da waje.

Sai dai Gwamnatin kasar ta bukaci hukumar Kwallon ta Malawi data bata ba’asin kudaden da aka kashe da ta baiwa hukumar a baya , wanda zuwa yanzu haka hukumar bata bada Rahoton ba.

Rashin bada rahoton ya sa gwamnatin kasar ta Malawi tace bata da kudaden da zata baiwa hukumar wajen cigaba da gudanar da shirin tunkarar wasan da zai gudana a watan Oktoba na 2021.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!