Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Muna bukatar bayanin rashin kokarin ‘yan wasan Najeriya a Tokyo 2020-Reps

Published

on

Majalisar wakilan kasar nan, ta ce za ta fara bincike kan musabbabin abinda ya faru a gasar motsa jiki ta Duniya da aka gudanar a Tokyo babban birnin Japan na 2020, wanda aka dakatar da wasu daga cikin yan wasan Najeriya.

Majalisar ta bukaci Ministan matasa da wasanni Sunday Dare da ya bayyana a gaban ta domin amsa tambayoyi game da yadda gasar ta gudana.

Tokyo Olympics: Najeriya ta bukaci ‘yan wasanta da su ciyo lambobin yabo

Majalisar ta ce ko kusa bata gamsu da yadda aka tafiyar da harkar wasannin ba wanda Nigeria ta halarta, inda ta ce akwai zarge zarge a ciki.

A yayin gasar dai kwamitin lura da gasar motsa jikin ta Tokyo ya ce an sami yan wasan Najeriya da karya ka’idar annobar covid 19, inda wasu daga cikin su suka shigo da takunkumin hanci da baki wari da wari

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!