Connect with us

Labaran Wasanni

Manchester na neman tsawaita kwantaragi da Pogba

Published

on

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Ole Gunnar Solskjaer, ya bukaci kara tsawaita kwantiragin dan wasa Paul Pogba da kungiyar, duba da karancin kudade da ake fama dashi sakamakon cutar COVID-19.

Mataimakin shugaban gudanarwar kungiyar Ed Woodward, ne ya gargadi hukumar gudanarwar ta Manchester United game da sayen ‘yan wasa, inda ya ce suna fama da karanci kudade a wannan lokacin bisa iftila’in cutar COVID-19.

Ed Woodward, ya ce, duba da irin kokarin da ‘yan wasan kungiyar ke yi tun farkon dawowa cigaba da wasanni a watan da ya wuce, hakan ya nuna cewa United ba ta da bukatar sayen ‘yan wasa idan an bude kasuwar cinikayyar ‘yan wasa a bana.

Ya kuma kara da cewa kwazon da dan wasa, Mason Greenwood, ya nuna wajen samun nasarar cin kwallaye 3 a wasanni guda 2, ya kara taimakawa wajen share maganar dauko dan wasan Borussia Dortmund, Jadon Sancho.

Ole Gunnar Solskjaer, ya ce, tun a lokacin da Paul Pogba ya dawo fagen fama daga jinya, ya yi sanadiyyar samun nasara a wasanni hudu tare da yin canjaras a wasa daya yayin da aka fara cigaba da wasanni bayan hutun COVID-19.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!