Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Manjo Janar Farouk Yahaya ya kama aiki a matsayin babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya

Published

on

Sabon babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya manjo janar Farouk Yahaya ya fara aiki a yau juma’a.

 

Rahotanni sun ce manyan janar-janar na rundunar ne suka yi maraba ga sabon babban hafsan sojin lokacin da ya isa shalkwatar tsaro ta ƙasa.

 

Ko da ya ke ba ayi kwarywa-kwaryar bikin da aka sabayi na mika ragamar aiki tsakanin babban hafsan da zai bar kan karagar aiki da wanda zai gaje shi ba, manjo janar Farouk Yahaya ya wuce ne kai tsaye zuwa ofishin babban hafsan tsaron kasa, Janar Lucky Irabor don tattaunawa.

 

Bayanai sun ce bayan fitowa daga ganawar sirri da babban hafsan sojin, laftanal janar Farouk Yahaya ya kuma tattauna da wasu manyan janar-janar na rundunar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!