Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Siyasa: Buhari ya yi wata ganawar sirri da Good Luck Jonathan

Published

on

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi wata ganawar sirri da tsohon shugaban ƙasa Good Luck Jonathan a fadar Asorok.

 

Rahotanni sun ce tattaunawar shugaba Buhari da Good Luck Jonathan ta mai da hankali ne kan rikicin siyasa da ke faruwa  a ƙasar Mali.

 

Ƙungiyar bunƙasa tattalin arzikin ƙasashen yammacin afurka ta ECOWAS dai ita ce ta naɗa tsohon shugaban na Najeriya Good Luck Jonathan a matsayin mai sasantawa a rikicin siyasa da ke faruwa a ƙasar ta Mali.

 

A cikin wata sanarwa da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Femi Adesina ya fitar, ta ce, shugaba Buhari ya kuma buƙaci ɓangarorin biyu da ba sa ga maciji da juna da su zauna teburi guda don sasanta saɓani da ke tsakaninsu

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!