Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Manjo Janar Taoreed ya karbi aiki a matsayin babban hafsin sojin Nijeriya

Published

on

Sabon babban hafsan sojin Nijeriya, Manjo Janar Taoreed Lagbaja, ya karɓi aiki a matasayin babban hafsan sojin ƙasa na 23, inda ya yi alkawarin sauke nauyin da aka ɗora masa bisa adalci.

Lagbaja ya karbi aiki ne a hannun Laftanar Janar. Faruk Yahaya wanda ke kan kujerar tun watan Mayun 2021.

A cewar sa ‘burin kowanne sojan yaƙi shi ne ya samu damar zama shugaban sojojin kasar nan’.

Laftanar Janar. Faruk ya kuma ce ‘zai yi la’akari da cancanta da aiki tuƙuru tsakanin dakarun sojin kasar, ta hanyar kyautata zamantakewa da abikannan aiki, tare da ɗaukar matakan da suka dace wajen dawo da wadanda suka kaucewa hanya a jagorancinsa’.

Rahoto: Yusuf Sulaiman Ahmad

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!