Coronavirus
Manoma 50,000 za su amfana da tallafin Corona a Najeriya
Gwamnatin tarayya ta ce fiye da kananan manoma dubu hamsin ne za su ci gajiyar tallafin rage radadin annobar cutar Corona na fadin kasar nan.
Karamin ministan noma da raya karkara, Mustapha Shehuri ne ya bayyana hakan yayin kaddamar da sabon shirin ga kananan manoma a kasuwar karshi dake birinin tarayya Abuja.
A cewar Mustapha Shehuri an fito da tsarin ne domin tallafawa kananan manoma domin rage musu radadi sakamakon annobar cutar Corona da ta addabi duniya.
Ministan ya kuma kara da cewa za a bi tsarin da ya dace domin tan-tance kananan manoman da za su ci gajiyar shirin tallafin .
Bankin raya kasashen Afrika ya ce, sama millyan Arba’in da tara na ‘yan kasashen Afrika za su fada cikin talauci, sakamakon cutar Corona a fadin duniya.
Wannan na cikin wani rahoton da bankin ke fitarwa mako-mako, na wannan shekara.
A cewar rahoton, kamata ya yi kasashen Afrika su bullo da dabarun farfado da tattalin arzikin su, musamman zuba jari a kananan kamfanoni, baya ga bai wa matasa tallafi domin rage musu radadin asarar da cutar ta hadassa.
Rahoton ya kuma ce, kamata ya yi kasashen Afrika su umarci dukkanin masana’antu da su bude domin bunkasa tattalin arzikinsu, tare da ci gaba da bin matakan da hukumomin lafiya suka bayar domin yakar cutar ta corona.
You must be logged in to post a comment Login