Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Manoma su guji amfani da dagwalon masana’antu a matsayin taki – Dakta Getso

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi manoman jihar da su guji yin amfani da dagwalon masana’antu a matsayin taki a gonakinsu.

Kwamishinan Muhalli, Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya yi wannan gargaɗi yayin taron masu ruwa da tsaki kan sha’anin muhalli.

Kwamishinan ya ce, amfani da dagwalon masana’antu a matsayin taki ga manoma yana da haɗari domin yana iya haifar da illa ga lafiyar al’umma ciki har da cutar ƙoda ga duk wanda ya ci amfanin noman.

Tsaftar muhalli: Za mu sake nazaratar duban kasuwanni a Kano

Dakta Getso ya ci gaba da bayanin cewa baya ga illa ga lafiya, dagwalon masana’antu ba shi da sinadarai masu gina jiki da za a yi amfani da shi a matsayin taki na gargajiya da zai bada yabanya mai kyau.

A cewar Kwamishinan, yankunan da galibin manoma ke yin wannan ta’ada ta amfani da dagwalon a matsayin taki sun haɗa da Wudil, Tamburawa, Dawakin Kudu, Gezawa, da dai sauransu.

Ya kuma yi kira ga mutanen da ke zaune a kusa da wuraren masana’antu irin su Sharada da Challawa da su yi taka-tsan-tsan don gujewa amfani da dagwalon masana’antun.

Dakta Getso ya kuma ce, nan ba da daɗewa ba ma’aikatar za ta fara wani gagarumin gangamin wayar da kan al’umma kan lamarin domin ceto da kuma kare rayukan al’ummar jihar.

Wanna dai na cikin sanarwar da mai magana da yawun ma’aikatar
Sunusi Abdullahi Ƙofar Nai’sa ya sanyawa hannu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!