Kasuwanci
Manoma su Jajircewa Noma a Damunar Bana- Sarkin Karaye
Sarkin Karaye Alhaji Ibrahim Abubakar na biyu, ya bukaci manoman da ke masarautar ta Karaye da su jajirce wajen Noma a damunar bana domin samar da abincin da ya kamata.
Alhaji Ibrahim Abubakar na biyu ya yi wannan kiran ne ya yin da ya ke mika tallafin irin shuka da babban bankin kasa CBN ya samar ga manoman masara a karamar hukumar ta karkashin kungiyar manoman masara da sarrafata da kuma kasuwancinta ta kasa wato Maize Growers Processors and marketers Association of Nigeria.
Sarkin na Karaye wanda ya samu wakilcin Alhaji Maikudi Aminu Santurakin karaye, ya kuma ja hankalin manoman da suka amfana da tallafin da su yi amfani da shi ta hanyar da ta da ce.
Da yake na sa jawabin shugaban kungiyar manoman masara ta kasa reshen jihar Kano (MAGPAMAN) Alhaji Yusuf Ado Kibiya, cewa ya yi yana da kyau kungiyoyin al’umma su kasance masu hadin kai domin samun gajiyar da ake samu na tallafin noma a kasar nan.
Bankin CBN ya bawa manoma bashi a Kano
Wasu daga cikin manoman da suka amfana da tallafin sun bayyana farin cikin su, inda suka ce za su yi amfani da tallafin bashin kayan noman da suka karba ta hanyar data dace.
Mai magana da yawun kungiyar ta manoman ta (MAGPAMAN) Sani Haruna Limawa, ya ce, mutane 145 ne za su amfana da tallafin da suka fito daga karamar hukumar ta karaye wanda kuma aka fara baiwa mutane 85 a Asabar 11 ga watan Yuli 2020.
You must be logged in to post a comment Login