Labaran Kano
Manoman jihar Kano sun mayar wa da CBN amfanin gona
Manoman jihar Kano sun fara mayar wa da babban bankin kasa CBN amfanin gonar da suka samu na noman auguda daga tallafin da bankin na CBN ya basu.
Manoman auduga da dama ne daga jihar Kano suka amfana da tallafin, wanda suka samu nasarar yin noman na auduga tare da samun riba mai yawa, inda suka mayar wa da bankin CBN amfanin gonar kamar yadda aka yi alkawari kafin a basu tallafin.
Da yake jawabi a wajen taron, mataimakin shugaban kungiyar masu noman auduga ta kasa shiyar arewa maso yamma Alhaji Munzali Dayyabu ya bayyana cewa samun nasarar wannan shiri ta ta’allaka ne ga irin gudunmawar da kungiyarsu ta bawa manoman, musamman ma a bangaren wayar musu da kai, inda ya kara da cewa, kungiyar ta su zata ci gaba da janyo bankuna da kamfanoni da manyan ‘yan kasuwa domin su tallafa a bunkasa noman auduga a kasa baki daya.
Da yake nasa jawabin jami’in da ya wakilci babban bankin kasa CBN a wajen taron Mista Azare ya bayyana gamsuwarsa ga yadda manoman jihar Kano suka yi amfani da bashin da aka basu ta hanyar da ta dace, wanda sanadiyar haka ne aka samu wannan nasara.
Ya kuma kara da cewa babban bankin Nigeria CBN zai ci gaba da tallafawa manoman auduga a kasa baki daya musamman ma na jihar Kano, duba da irin nasarar da shirin ya samu a wannan lokacin.
Wasu daga cikin manoman da suka amfana da wannnan tallafi kuma suka samu nasarar dawo da amfanin gonar sun godewa bankin na CBN, inda suka a shirye suke su ci gaba da kulla alaka da bankin ta hannun babbar kungiyar manoman auduga ta kasa