Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Manu Garba ya zama sabon mai horar da kungiyar Golden Eagles- NFF

Published

on

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya (NFF) ta nada Manu Garba a matsayin sabon mai horar da kungiyar kwallon kafa ta kasa Matasa ‘yan kasa da shekaru 17 Golden Eaglets, a matsayin sabon mai horar da ‘yan wasan ta.

Hakan na cikin wata sanarwa da Daraktan yada labaran kungiyar Ademola Olajire, ya fitar a yau Juma’a 12 ga watan Afrilun shekarar 2024.

Manu Garba, dai shene mai horarwar da ya dauki kungiyar ta Golden Eaglet wajen lashe gasar cin kofin Duniya ta ‘yan kasa da shekaru 17 da aka gudanar a hadaddiyar daular Larabawa UAE a shekarar 2013.

Ademola Olajire ta cikin sanarwar ya kuma ce Manu Garba zai fara aikin horar da ‘yan wasan ba tare da bata lokaci ba, musamman domin ci gaba da shirye-shiryen da ta ke na fafata gasar cin kofin kasashen ‘yanmacin Afrika ta WAFU B da za a fafata a kasar Ghana a wata mai kamawa na Mayu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!